logo

HAUSA

Jami’in AU: An samu raguwar yaki da ta'addanci a Afirka saboda rashin goyon bayan kasa da kasa

2022-05-30 09:37:08 CMG Hausa

Shugaban hukumar gudanarwar kungiyar Tarayyar Afirka (AU) Moussa Faki Mahamat ya bayyana cewa, an samu raguwar yaki da ayyukan ta’addanci matuka a nahiyar Afirka, sakamakon rashin cikakken goyon baya daga kasashen duniya.

Mahamat ya bayyana hakan ne ranar Asabar din da ta gabata, yayin da shugabannin kasashen Afirka ke gudanar da babban taron kolin kungiyar ta AU kan ayyukan ta'addanci da sauye-sauyen gwamnatin da suka sabawa kundin tsarin mulki a Afirka da aka gudanar a Malabo, babban birnin kasar Equatorial Guinea.

Taron ya yi hasashen karfafa tsaro tare da kasashen Afirka da ke fuskantar ayyukan ta'addanci da sauye-sauyen gwamnati da ba su dace ba.

Mahamat ya bayyana cewa, ta'addanci da sauye-sauyen gwamnati ba bisa ka'ida ba, suna taimakawa juna, gami da wasu dalilai masu nasaba da haka, wadanda ke bayar da dama ga yin juyin mulkin soji da hare-haren ta'addanci a nahiyar.

Jami’in na AU ya bayyana cewa, an samu tafiyar hawainiya a yakin da ake yi da ta'addanci a nahiyar Afirka, saboda rashin kwakkwaran jajircewa daga kasashen duniya.

Ya kuma bayyana damuwarsa kan sake bullar juyin mulkin da sojoji suke yi a nahiyar Afirka, inda ya jaddada bukatar kawar da sauye-sauyen gwamnati da suka sabawa kundin tsarin mulki a Afirka, domin hakan, shi ke haddasa yawaitar ayyukan ta'addanci da tashe-tashen hankula masu nasaba da makamai. (Ibrahim)