logo

HAUSA

Tattalin Arzikin Sin 2022: Akwai Yiwar Tattalin Arzikin Sin Ya Bunkasa Fiye Yadda Ake Hasashe

2022-05-30 18:43:15 CMG HAUSA

Masu azancin magana na cewa, “Juma’ar da za ta yi kyau, tun daga Laraba ake ganewa.” Da alama za mu iya cewa hasashen da masana suka yi game da yiwuwar samun tagomashin bunkasar tattalin arzikin kasar Sin ya fara tabbata, domin kuwa, a kwanakin baya bayan nan da suka gabata, dukkanin larduna da birane 31 na kasar Sin sun fitar da ma’aunin ci gaban tattalin arzikinsu na GDP a rubu’in farko na bana, inda alkaluma suka nuna cewa, sassa daban daban na kasar sun samu ci gaba mai inganci yadda ya kamata, duk da cewa ana fama da matsin lamba da sauye-sauyen yanayin da ake fuskanta na cikin gida da na kasa da kasa.

A cikin watanni uku na farkon bana, adadin GDP na larduna 11 da suka hada da lardin Guangdong ya zarta kudin Sin yuan triliyan daya, amma a makamancin lokacin bara, lardunan da adadin GDPn su ya zarta triliyan daya 8 ne kawai. Kana game da saurin ci gaban tattalin arzikin kuwa, ban da lardin Jilin wanda a baya bayan nan ya fuskantar tasirin yaduwar annobar COVID-19, sauran larduna da birane 30 dake fadin kasar sun samu karuwar tattalin arziki a rubu’in farkon bana, inda wasu lardunan dake tsakiya da yammacin kasar wadanda suka hada da Hubei da Shanxi da Xinjiang da Guizhou suka samu ci gaba cikin sauri har saurin ya kai kaso 6 bisa dari bisa makamancin lokacin bara.

Mataimakin shugaban cibiyar nazarin tattalin arziki bisa manyan tsare-tsare ta kasar Sin Wu Sa, ya bayyana a kwanan baya cewa, duk da cewa tattalin arzikin yankunan gabashin kasar ba su samu ci gaba cikin sauri ba, amma suna samun ci gaba mai inganci. Duk da barazana da kalubaloli daban daban da ta fuskanta, kasar Sin ta ci gaba da farfado da tattalin arzikinta. Kana ta cimma manyan manufofinta yadda ya kamata. Jimillar tattalin arzikin kasar Sin a bara ya kai dalar Amurka triliyan 3, wanda ba a taba ganin irinsa ba a tarihin duniya. Aiki ne mai wahala da kasar Sin ta kai ga cimma kyawawan sakamako. Hakan ya nuna cewa, kasar Sin na da karfin juriya wajen raya tattalin arziki, tana daidaita barazana yadda ya kamata, kana kuma hakan na da nasaba da yadda take yaki da annobar COVID-19, da kuma dora muhimmanci kan samun ci gaban tattalin arziki da zamantakewar al’ummar kasa ba tare da tangarda ba.

Kasar Sin ta sanya burin daga yawan GDPn kasar da kaso 5.5 bisa dari a shekarar 2022. Ta yi tunani mai zurfi kan halin da take ciki a gida da waje ta fuskar bunkasa tattalin arziki, kana adadin ya dace da hakikanin yanayin bunkasar tattalin arziki. Dama dai masu hikimar magana na cewa, “Juma’ar da za ta yi kyau, daga Laraba ake ganewa.” (Ahmad Fagam)