logo

HAUSA

Shugaban AU ya bayyana damuwa kan batun agajin gaggawa a Afrika

2022-05-29 17:05:20 CMG HAUSA

 

Moussa Faki Mahamat, shugaban gudanarwar kungiyar tarayyar Afrika AU, ya bayyana cewa, samar da tallafin jin kai na gaggawa, wani babban abin damuwa ne a nahiyar Afrika.

Mahamat ya bayyana hakan ne a yayin taron kolin AU na musamman game da ayyukan jin kai da alkawurra, wanda aka gudanar a Juma’ar da ta gabata, inda ya bayyana cewa, bukatun ayyukan jin kai da ake da su a Afrika suna da matukar yawa, kuma sun shafi bangarori da shiyyoyi da dama, sannan sun kasance a matsayin wani babban abin damuwa.

Ya kara da cewa, cikin kasashe 15 mambobin AU da matsalar ta fi kamari, akwai mutane miliyan 113 dake jiran tsammanin tallafin jin kan gaggawa a shekarar 2022.

Mahamat ya ci gaba da cewa, a gabashin Afirka da kusurwar Afrika, a halin yanzu akwai mazauna sansanonin ‘yan gudun hijira kimanin miliyan 4.5, sama da kashi 75 bisa kashi dari na adadin sun fuskanci matsalar raguwar tallafin abincin da ake ba su a shekarar 2021.

Ya nuna cewa, a shekaru biyu da suka gabata, adadin bukatar abincin da ake da ita ya karu da kashi 70 bisa kashi100 a gabashin Afirka da kusurwar Afrika, sannan sama da mutane miliyan 25 suna cikin yanayin karancin abinci.

Mahamat ya ce, a yammaci da tsakiyar Afrika, akwai mutane miliyan 58 dake fama da matsalar karancin abinci, wanda shi ne adadi mafi yawa na karancin abinci da aka taba fuskanta tun daga shekarar 2016.(Ahmad)