An kammala taron kolin Afrika kan koffi tare da alkawarin bunkasa cinikayyar hajar
2022-05-29 16:43:46 CMG Hausa
Da yammacin ranar Juma’a aka kammala taron kolin kasashen Afrika kan koffi na tsawon kwanaki uku a Nairobi, babban birnin kasar Kenya, inda mahalartan suka yi alkawarin bunkasa cinikayyar koffin a fadin nahiyar.
Sama da wakilai 500 da suka halarci taron kolin, sun bayyana cewar, cinikayyar koffi a tsakanin kasashen Afrika zai yi matukar bunkasa cigaban kasuwanci a nahiyar, sannan zai samar da sabbin guraben ayyukan yi, kana zai kara bunkasa hada-hadar musayar kudaden waje.
Wakilan sun bunkaci gwamnatoci da su yi kokarin samar da ingantaccen muhallin cinikayyar koffi, ta hanyar bullo da ingantattun manufofi, da fadada ayyukan hidimomi, da amincewa da muhimman shawarwarin da ake gabatarwa, da kyautata fannin sufuri, da kuma kawar da shinge a tsarin cinikayya.
Mahalartan, wadanda suka fito daga kasashen Afrika 25, sun bukaci a daidaita dokoki, da aiwatar da manufofi masu inganci, wadanda za su taimaka wajen bunkasa cinikayyar koffi.
Solomon Rutega, sakatare janar na kungiyar hada-hadar koffi a tsakanin kasashen Afrika (IACO), ya bukaci kungiyoyin shiyya-shiyya da su yi kokarin daidaita manufofi, da matakai, da kuma ma’aunai don ba da taimako wajen inganta harkokin cinikayyar shiyya-shiryya da tabbatar da inganci.(Ahmad)