logo

HAUSA

‘Yan bindiga sun kashe mutum guda da yin garkuwa da wasu biyar a arewacin Najeriya

2022-05-29 16:41:11 CMG Hausa

 

A kalla mutum guda aka kashe sannan wasu mutanen biyar aka yi garkuwa da su yayin da wasu ‘yan bindiga da ba a tantance ko su wanene ba suka kaddamar da hari a wani kauyen jihar Kaduna a arewacin Najeriya a ranar Asabar, kamar yadda wata majiyar ‘yan sanda ta bayyana hakan.

A cewar majiyar daga wani jami’in dan sandan, wanda ya nemi a sakeye sunansa, saboda ba a ba shi iznin tattaunawa da ‘yan jaridu ba, ya fadawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, maharan sun kaddamar da harin ne da sanyin safiyar ranar Asabar a kauyen Jere dake karamar hukumar Kagarko a jihar Kaduna, inda suka kashe wani ango da bai jima da aure ba, kana suka yi awon gaba da matarsa mai dauke da juna biyu.

Ya kara da cewa, ‘yan bindigar sun kuma yi awon gaba da mutane hudu iyalan wani tsohon jami’in jihar dake zaune a kauyen.(Ahmad)