AfDB: za a sanya salon tattalin arziki mai amfani da makamashi mai tsafta cikin fasalin raya nahiyar Afrika
2022-05-28 16:13:17 CMG Hausa
Bankin raya Afrika AfDB, ya bayyana cewa, za a sanya salon raya tattalin arziki dake kunshe da bunkasa ayyukan masa’antu ta hanyar sake sarrafa kayayyaki da amfani da makashi mai tsafta cikin fasalin raya tattalin arzkin nahiyar.
Mataimakin shugaban bankin a bangaren kula da makamashi da sauyin yanayi da raya muhalli Kevin Kariuki ne ya bayyana haka yayin taron shekara-shekara na bankin.
A cewarsa, sake juya kayayyakin da ake sarrafawa na da muhimmanci ga farfadowar nahiyar daga tasirin COVID-19 cikin sauri, domin samar da sabbin guraben ayyukan yi a wani yanayi mai dorewa a nahiyar.
Ya ce sauyawar nahiyar zuwa mai raya muhalli ta hanyar amfani da makamshi mai tsafta, wani mataki ne na bin alkiblar da ta dace na samar da sabon tsarin darajar kayayyaki da zai bunkasa tattalin arzki da samar da sabbin guraben ayyukan yi masu dorewa.
Bankin ya bude taron nasa na shekara na 2022 ne ranar Talata a Accra babban birnin Ghana, inda ya samu halatar dattijan nahiyar da ‘yan siyasa da masana. (Fa’iza Mustapha)