logo

HAUSA

Jakadan Sin dake Najeriya ya gana da janar Gowon

2022-05-28 15:27:48 CMG Hausa

Jakadan kasar Sin a tarayyar Najeriya Cui Jianchun, ya gana da tsohon shugaban gwamnatin sojan kasar Yakubu Gowon, wanda ya taba ba da gagarumar gudummowa ga ci gaban huldar diplomasiyyar tsakanin kasashen biyu.

Jakada Cui ya bayyana cewa, a halin yanzu, huldar dake tsakanin Sin da Najeriya tana gudana yadda ya kamata karkashin kokarin da gwamnatoci da al’ummomin sassan biyu suke yi, kana kasashen biyu suna goyon bayan juna a fannin siyasa, kuma suna taimakawa juna wajen ci gaban tattalin arziki da cinikayya. Ya ce a nan gaba, kasar Sin tana son hada hannu da Najeriya domin tabbatar da sakamakon da aka samu yayin taron ministoci karo na 8 na dandalin tattauna hadin gwiwar Sin da kasashen Afirka, tare kuma da ciyar da huldar dake tsakanin sassan biyu gaba.

A nasa bangaren, janar Gowon ya bayyana cewa, “Kasar Sin da al’ummun Sinawa dake karkashin jagorancin JKS, sun samu babban sakamako wajen gina kasarsu, na taba ziyartar kasar Sin sau da dama a shekarun 1980 da na 1990, da idona na ga yadda kasar Sin ta sauya daga kasar aikin gona dake fama da koma baya, zuwa kasar masana’antu mai wadata. Ya dace kasashe masu tasowa kamar Najeriya su koyi fasahohin gudanar da harkokin kasa irin na kasar Sin. Hakika a cikin ‘yan shekarun da suka gabata, tarayyar Najeriya ita ma ta samu babban ci gaba a fannin raya tattalin arziki da zamantakewar al’umma, mun godewa kasar Sin saboda goyon bayan da take ba ci gaban Najeriya a fannoni daban daban.” (Jamila)