logo

HAUSA

Sabuwar manufar Amurka kan Sin ba ta canja tunaninta na yakin cacar baka da fin karfi ba

2022-05-28 15:25:53 CMG Hausa

Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken, ya gabatar da wani jawabi game da manufar kasarsa kan kasar Sin a jami’ar George Washington a ranar 26 ga wata, inda ya bayyana cewa, Amurka tana aiwatar da manufar “zuba jari da hada kai da yin takara” kan kasar Sin, amma kafin hakan, ya taba bayyana cewa, manufar ita ce: “takara da hadin gwiwa da nuna kiyayya”. Duk da cewa, akwai bambanci kadan tsakaninsu, ainihin yanayin da Amurka ke ciki shi ne, ta gamu da cikas yayin da take matsawa kasar Sin lamba. Amurka ba ta sauya tunaninta na yakin cacar baka da nuna fin karfi ba, sai dai sauya dabarunta na hana ci gaban kasar Sin kadai.

A cikin jawabinsa, Blinken ya sake yada karairayin wai kasar Sin tana kawo wa tsarin kasa da kasa babban kalubale mai dorewa. Hakika wadda ke kawo wa tsarin kasa da kasa kalubale mai tsanani ita ce Amurka. Ga misali, kai wa Iraki hari, da tayar da yakin basasa a Libya da Syria, da ficewa daga yarjejeniyar makaman nukiliya ta Iran, da barkewar rikicin Ukraine, sakamakon sa kaimi kan Nato ta fadada zuwa gabashi, da kitsa kiyayya tsakanin kasa da kasa. Duk wadannan sun nuna cewa, Amurka ce ke zaman kalubale mafi girma ga zaman lafiya da kwanciyar hankalin kasashen duniya. (Jamila)