logo

HAUSA

Afrika ta damu da rashin masu sayen alluran riga kafin COVID-19 daga masu samar da ita a nahiyar

2022-05-27 11:58:07 CMG Hausa

Cibiyar kandagarki da dakile yaduwar cututtuka ta nahiyar Afrika, Africa CDC, ta bayyana damuwa game da rashin kasuwa da masu samar da alluran riga kafin COVID-19 a nahiyar ke fama da shi.

Mukaddashin daraktan cibiyar Africa CDC, Ahmed Ogwell ne ya bayyana damuwar, yana mai jaddada bukatar tabbatar da kasuwa mai dorewa ga masu samar da riga kafi na nahiyar, bisa la’akari da cewa, nahiyyar ce mafi bukatar alluran riga kafin.

Tsokacin na Ahmed Ogwell na zuwa ne yayin da masu samar da alluran riga kafi a nahiyar ke bayyana damuwa kan rashin kasuwar, suna barazanar rufe cibiyoyin sarrafa riga kafin saboda rashin oda.

Matsalar ta zo duk da har yanzu nahiyar ce ke da mafi karancin wadanda aka yi wa allurar riga kafin cutar a duniya, inda kaso 16.5 na al’ummarta ne kadai suka samu cikakkiyar allurar. (Fa’iza Mustapha)