logo

HAUSA

A kalla mutane 50 sun mutu a harin Burkina Faso

2022-05-27 10:29:27 CMG Hausa

A kalla mutane 50, mazauna Madjoari dake gabashin Burkina Faso ne suka mutu a ranar Laraba, sanadiyyar wani hari da aka kai musu.

Gwamnan yankin Gabas na Burkina Faso, Hubert Yameogo, ya bayyana cikin wata sanarwa cewa, wasu ’yan bindiga da ba a san ko su wane ne ba, sun farwa mutanen na garin Madjoari dake kokarin isa Nadiagou, wani gari a yankin Pama na kasar.

Hubert Yameogo, ya kuma jajantawa iyalan wadanda harin ya rutsa da su, yana mai cewa yanzu haka, jami’an tsaro na gudanar da ayyukan da suka kamata. (Fa’iza Mustapha)