logo

HAUSA

GCA za ta taimakawa Ghana wajen samun dala biliyan 1.3 don aiwatar da matakan dakile sauyin yanayi

2022-05-27 11:57:02 CMG Hausa

Cibiyar kasa da kasa mai tallafawa ayyukan dakile mummunan tasirin sauyin yanayi ta GCA, ta alkawarta taimakawa kasar Ghana, ta yadda kasar za ta samu kudaden da yawan su ya kai a kalla dalar Amurka biliyan 1.3, domin aiwatar da matakan dakile tasirin sauyin yanayi.

Babban shugaban GCA Patrick Verkooijen, shi ne ya tabbatar da hakan a jiya Alhamis yayin taron manema labarai, yana mai cewa, yana da muhimmanci ga wannan kasar dake yammacin Afirka, ta samu kudaden gudanar da kudurorin su na dalike tasirin sauyin yanayi, ta hanyar gina ababen more rayuwa masu nasaba da hakan.

Mr. Verkooijen ya ce, tuni GCA ta fara aiki da gwamnatin kasar Ghana, wajen gina tsarin samar da ababen more rayuwa, wadanda za su taimakawa kasar samar da ruwan sha mai tsafta, da inganta samar da makamashi, da fadada hidimomin sufuri, da samar da karin guraben ayyukan yi.   (Saminu)