logo

HAUSA

Ziyarar Michelle Bachelet Shaida Ce Cewa Kasar Sin Ba Ta Da Abun Boyewa

2022-05-26 21:28:53 CMG HAUSA

Batun kare hakkin dan Adam batu ne mai muhimmanci ga al’ummar duniya. Sai dai, wasu na fakewa da shi wajen yayata manufarsu da ingiza rikici da ta da zaune tsaye. 

A jiya ne shugabar hukumar kare hakkin dan Adam ta MDD, Michelle Bachelet ta fara ziyara a kasar Sin, inda za ta ziyarci lardunan Guandong da kuma jihar Xinjiang ta Uygur mai cin gashin kanta. 

Kasar Sin ta shafe shekaru da dama tana fuskantar suka daga kasashen yamma ta hanyar ruruta batun kare hakkin dan Adam a kasar, musammam ma a jihar Xinjiang.

Kasar Sin ta sha nanata cewa tana maraba da jami’ai daga wadannan kasashe da ba su taba ganin yanayin jihar Xinjiang ba, su ziyarci jihar don ganewa idanunsu yadda al’umma suke rayuwa cikin yanayin na kwanciyar hankali da wadata.

Ziyarar Michelle Bachelet, na zaman shaidar cewa, da gaske kasar Sin take, kuma  ba ta da abun boye dangane da yanayin da al’ummarta ke ciki. Duk wanda ke bibbiyar yanayin kasar Sin ko ya ziyarci kasar, ya san cewa, tana dagewa wajen tabbatar da kare al’ummarta. Kana ba ta taba musanta daukar mataki kan ’yan ta’adda a jihar Xinjiang ba, matakan da kawo yanzu suka haifar da da mai ido ta hanyar tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankalin al’ummar yankin. Kazalika, sun samu goyon baya daga kasashen musulmi da ma wadanda suke fuskantar hare-haren ta’addanci.

Fatan a yanzu shi ne, wannan ziyara ta shugabar hukumar kare hakkin dan Adam, za ta kara fahimtar da al’ummar duniya manufar kasashen yamma kan Sin, kuma shugabar za ta fayyace ainihin abun da ta gani domin wanke Sin din daga zarge-zarge marasa tushe da ake mata. (Faeza Mustapha)