Gwamna: Yan ta’adda sun kashe gomman mutane a arewa maso gabashin Najeriya
2022-05-26 11:18:33 CMG Hausa
Wani gwamnan jaha a Najeriya ya tabbatar a ranar Laraba cewa, mayakan ’yan ta’adda masu tsattsauran ra’ayi sun kashe mutane da dama, a hari na baya bayan nan da suka kaddamar kan wani kauyen dake jahar Borno, a shiyyar arewa maso gabashin kasar.
Babagana Umara Zulum, gwamnan jahar Borno mai fama da tashe-tashen hankulla, ya bayyana cewa, a ranar Asabar mayakan ’yan ta’addan Boko Haram da na ISWAP, sun bude wuta tare da kashe mutane da dama a yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa wani kauyen dake karamar hukumar Kala Balge a jahar.
Gwamnan ya yi Allah wadai da harin, inda ya bayyana kashe-kashen a matsayin abin takaici, wanda ya hana shi sukuni a karshen wannan mako. Ya bayyana cewa, gwamnatin jahar tana jiran samun cikakken rahoto game da harin.
Ya kara da cewa, kawo yanzu, tawagar rundunar sojoji ta gano gawarwakin wasu daga cikin mutanen da harin ya rutsa da su, inda ya ce, alamu sun nuna an daure mutanen sannan aka harbe su.
A cewar gwamnan, wadanda harin ya rutsa da su, mutane ne dake sana’ar tattara tarkacen karafuna. Kuma an kai musu harin ne a yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa kauyen don neman karafunan. (Ahmad)