logo

HAUSA

Shugabar kasar Tanzania: AfCFTA na tattare da damar bunkasa nahiyar Afirka

2022-05-26 11:33:17 CMG Hausa

Shugabar kasar Tanzania Samia Suluhu Hassan, ta ce yarjejeniyar cinikayya maras shinge ta Afirka ko AfCFTA, na tattare da manyan damammaki na raya ci gaban nahiyar Afirka.

Shugaba Samia ta yi wannan tsokaci ne a jiya Laraba, lokacin da ta ziyarci sakatariyar yarjejeniyar ta AfCFTA. Ta ce sassan yarjejeniyar sun tanadi damammaki na ingiza hada hadar cinikayya tsakanin sassan Afirka, da ma hanyoyin gudanar da su bisa tsari mafi dacewa, wanda hakan ko shakka babu zai ingiza dorewar ci gaban bunkasuwar Afirka.

Shugabar ta Tanzaniya ta ce "Yayin da kasashen Afirka ke farfadowa daga komadar tattalin arziki sakamakon bazuwar annobar COVID-19, aiwatar da yarjejeniyar AfCFTA za ta gaggauta murmurewar su, duba da yadda yankunan cinikayyar suka hade al’ummun da yawansu ya kai miliyan 1.2".

Da yake maraba da shugabar kasar, babban sakataren sakatariyar AfCFTA Wamkele Mene, ya ce ziyarar ta dada tabbatar da himmar shugabannin Afirka, game da burin ganin an cimma nasarar aiwatar da yarjejeniyar yadda ya kamata. (Saminu)