Wasu 'yan siyasar Japan na neman cin amanar Asiya
2022-05-26 20:47:41 CMG Hausa
A kwanakin baya ne, shugabannin kasashe hudu da suka hada da Amurka da Japan da Indiya da kuma Australia, suka gudanar da wani taro da ake kira "Quad Mechanism" ko (QUAD) a birnin Tokyo na kasar Japan, inda firaministan Japan Fumio Kishida ya jagoranci taron. Ko da yake sanarwar hadin gwiwa da aka fitar bayan taron, ba ta ambaci sunan kasar Sin ba, amma rahotannin kafafen yada labarai na kasar Japan, sun nuna alkiblar kungiyar kasashen. Dangane da tattaunawar da shugabannin kasashen Japan da Amurka suka yi, da kuma munanan kalamai da ayyuka da suka shafi kasar Sin a cikin sanarwar hadin gwiwa tsakanin Japan da Amurka, wasu 'yan siyasar Japan suna janyo abin da zai haifar da rikici, da haddasa yin fito na fito, da yadda ake yin “maraba da Amurka da neman cin amanar Asiya" yana kara fitowa fili. (Ibrahim)