logo

HAUSA

Huawei ya fadada horaswa kan fasahar ICT don samar da kwararru a Kenya

2022-05-26 11:27:57 CMG Hausa

Kamfanin sadarwa na Huawei ya fadada shirinsa na bada horo kan fasahar sadarwa ta zamanin ICT, da zummar samar da kwararru a kasar Kenya, kamar yadda jami’in kamafanin ya bayyana.

Dalmar Abdi, babban jami’in sashen hulda da jama’a na kamfanin Huawei Kenya, ya bayyana a Nairobi babban birnin kasar Kenya cewa, shirin bada horon wanda cibiyar bada horo ta kamfanin Huawei ta shirya, ta yi hakan ne domin cike gibin horo a fannin fasahar zamani ta ICT a kasar Kenya.

Abdi ya ce, domin cimma wannan buri sun yi hadin gwiwa da wasu cibiyoyin ilmi mai zurfi 80, domin koyar da dalibai hakikanin fasahar zamani ta ICT, domin ilmantar da su ta hanyar na’urorin zamani.

Cibiyar bada horo ta Huawei, tamkar wani gida ne dake daga matsayin fasahar sadarwar zamani na Afrika wato (AFRALTI) a Nairobi, kuma ana fatan za ta bayar da horo na matsayin koli ga wasu kwarru a kalla 200 kan fasahar ICT, da kuma karin horar da wasu kimanin 5,000 a fasahar ICT.

Ya bayyana cewa, kamfanin fasahar na kasar Sin yana burin horar da wasu ma’aikatan gwamnati 2,500, da wadanda suka kammala karatu kimanin 12,000, da matasan dalibai a kasar Kenya. (Ahmad)