logo

HAUSA

AU: Afirka na dandana mummunan tasirin rikicin Ukraine

2022-05-26 11:19:40 CMG Hausa

Shugaban hukumar gudanarwar kungiyar tarayyar Afirka ta AU Moussa Faki Mahamat ya ce, kasashen nahiyar Afirka na matukar dandana kudar su, sakamakon mummunan tasirin rikicin dake gudana tsakanin Rasha da Ukraine.

Cikin wata sanarwar da aka fitar a jiya Laraba, Mahamat ya ce rikicin Ukraine ya wargaza daidaiton dake akwai tsakanin sassan yankunan duniya, ya kuma dada fito da raunin tsarin tattalin arzikin Afirka a fili.

Jami’in ya ce wannan rikici, ya tauye damar da ake da ita ta fitar da amfanin gona zuwa sassan duniya, ya kuma ta’azzara hauhawar farashin kayayyakin abinci.

Ya ce baya ga kalubalen sauyin yanayi, da annobar COVID-19, rikicin Ukraine ya sake ingiza matsalolin karancin cimaka da duniya ke fama da shi.

Wani rahoto da shirin samar da ci gaba na MDD ko UNDP ya fitar a ranar Talata, ya yi gargadin cewa, rikicin Ukraine na iya kara tsananta koma bayan ci gaban kasashen Afirka, kasashen da tuni suke shan matsi daga tasirin annobar COVID-19.  (Saminu)