logo

HAUSA

Kwallo mai sauti tana farfado da burin yara masu larurar gani

2022-05-26 20:30:36 CMG Hausa

Wata nauyin kwallon kafa mai fitar da amo daga cikin ta da aka kirkira, tana jan hankalin dubban yara masu larurar gani a sassan duniya. Cikin shekaru 4 da suka gabata tun bayan kirkirar wannan kallo, yara masu larurar gani sun samu karsashi na yin wasan kwallon kafa tare da takwarorin su masu gani sosai, inda suke taka leda cike da nishadi, da irin wannan nau’in kwallon kafa.

‘Yar karamar kwallo "Ta kowa da kowa"

Nau’in wannan kwallo ta yara dai bai wuce garam 250 ba, kasa da ta baligai masu larurar gani wadda ta kai nuyin giram 550. Elias Mastoras, shugaban hadaddiyar hukumar dake lura da wasannin mutane masu larurar gani ko IBSA, kuma jagoran kungiyar tallafawa masu larurar gani ta “Youthorama” mai helkwata a birnin Thessaloniki, dake gabar tekun arewacin kasar Girka, shi ne ya kirkiri wannan kwallo.

Bisa gangamin kasa da kasa na "Kwallo ga kowa," wanda kawo yanzu ya samar da irin wannan sabuwar nau’in kwallo har 8,500 ga yara dake kasashe da yankunan duniya har 213, hakan ya sanya hukumar gudanarwa ta tarayyar turai, ta karrama wannan kungiya ta “Youthorama” dake Girka a watan Mayu, da lambar shekara shekara ta “Be Inclusive EU Sport”.

Yayin wata zantawa da ya yi da kamfanin dillancin labarai na Xinhua, Mr. Mastoras ya ce wannan karramawa ta karfafa masa gwiwar ci gaba da dora muhimmanci, ga aikin tallafawa masu rauni cikin al’umma, kamar dai wannan aji na masu larurar gani, ta yadda za su shiga a dama da su a fannin wasanni.

Mastoras ya ce "Mafi yawan yara masu larurar gani suna zuwa makarantun gama gari ne. Kuma a irin wadannan makarantu, akan ware yara masu larurar gani, amma a yanzu da ake da wannan sabuwar nau’in kwallo, yara masu larurar na iya taka leda tare da sauran yara.

Ya ce "Hakan na taimaka musu ba kawai a lokutan karatu ba, har ma da yadda suke da dama a yanzu ta yin wasa tare, ana kara gayyatar su a lokutan karshen mako domin yin wasa tare da sauran yara.

Mene ne tushan wannan hikima

Mastoras ya tuna gamuwar sa da wani yaro mai larurar gani dan shekaru 4, mai suna Leandros a shekarar 2017, a wata makaranta ta makafi dake Thessaloniki, haduwar da ta sauya tuananin Mastoras.

Da farko Mastoras ya baiwa Leandros wata kwallon kafa, da niyyar ta ya rika wasa tare da ‘yar uwarsa, amma sai ya lura cewa kwallon ta yiwa yara nauyi.

Don haka Mastoras, wanda ke cikin harkar wasan kwallon kafar makafi tun daga shekarun 1990, ya yanke shawarar kirkirar karamar kwallo, wadda za ta dace da yanayin yara makafi da masu larurar gani. Irin wannan kwallo dai ba a sayar da ita a shaguna, sai dai kawai ana samar da ita ne ta hanyar tallafin da kungiyar ke samarwa yara.

Wannan fasaha ta riga ta samu tallafin gwamnatoci, da kungiyar tarayyar turai ta EU, da kulaflikan wasanni da wasu hukumomi, kamar asusun yara na UEFA, da masu daukar nauyin wasanni, da sanannun ‘yan kwallo, da masu horas da kwallo dake sassan duniya daban daban.

Akwai babbar bukatar wadannan kwallo

A sassan duniya baki daya bisa kiyasi, akwai mutane masu larurar gani da yawan su ya kai miliyan 285, ciki har da makafi miliyan 39, da masu larurar karancin gani miliyan 246, yayin da kiyasin kungiyar “Youthorama” ya nuna akwai yara kanana kimanin 500,000 dake makancewa a duk shekara.

Kwallon kafa mai sauti ta isa filin wasan da aka buga gasar kwallon kafa ta EURO 2020

A ‘yan watanin baya, da tallafin asusun yara na hukumar UEFA, yara 30 sun isa birnin Budapest, kafin a take wasan EURO 2020 tsakanin Faransa da Portugal, yaran sun nuna fasahohin su na kwallon kafa da kwallo mai sauti ga ‘yan kallo.

A watan Afirilu, hukumar UEFA ta zabi Leandros, wanda a yanzu ya kai shekaru 9, domin ya kaddamar da wasan kusa da kusan na karshe na gasar UEFA, tsakanin kungiyar PAOK da Marseille a Thessaloniki.

Wannan ne lokaci na farko da Leandros ya taba shiga filin wasan kwallon kafa. ‘Yan kwanaki bayan nan kuma, sai kungiyar PAOK ta sake gayyatarsa zuwa filin wasa, inda ya jefa kwallo a raga, gabanin wasan da kungiyar za ta buga.

Cike da murna, Leandros ya daga murya yana cewa "Na gode sosai" yayin da dubban ‘yan kallo ke shewa suna jinjina masa.