logo

HAUSA

Kasashen Yamma Na “Fakewa Da Guzuma Domin Harbin Karsana”

2022-05-26 21:30:23 CMG HAUSA

Sau da yawa wasu kasashen yammacin duniya, suna danganta ci gaban da suka samu da biyayyar su ga tsarin dimokaradiyya, da salon mulki mai alaka da hakan.

Ga misali, kasashen Amurka da Birtaniya, da kasashen tarayyar Turai, na yayata cewa dimokaradiyya ce ta haifarwa al’ummunsu da daidaito wajen samun damammakin kyautata rayuwa da 'yanci, kuma hakan ne ya ba su damar bunkasa tattalin arzikin su yadda ya makata. Don haka ne suke tsananin fatan yayata salon jagorancin su zuwa sauran sassan duniya.

To sai dai kuma, masu sharhi kan al’amuran siyasar duniya da dama, na ganin cewa, wannan ikirari ba gaskiya ba ne. Hasali ma ci gaban da dama daga kasashen yamma, ya dogara ne ga yadda gwamnatocinsu na can baya, suka ci da gumin kasashe masu rauni. Hakan na iya kara bayyana, idan aka yi waiwaye kan yadda irin wadannan kasashen yamma suka bautar da wasu al’ummun kasashen Asiya, da na Latin Amurka, da na Afirka, suka kuma wawure albarkatun su.

Ko shakka babu, yayata dimokadiyya salon kasashen yamma, wata dabara ce ta yaudara, da “fakewa da guzuma a harbi karsana”. Hanya ce ta samarwa kai moriyar tattalin arziki, da sarrafa ikon kasashe musamman masu rauni.

Abubuwan da suka faru bayan yakin duniya na biyu, na mamayar kasashe da karfin soji, da mulkar kasashe ta amfani da 'yan koren kasashen yamma, da rura wutar yake yake, da kifar da zababbun gwamnatoci, da kafa hukumomin kudi masu dorawa kasashe bashi mai ruwa fiye da kima, dukkanin su shaidu ne, na yadda wadannan irin manyan kasashen yammacin duniya suka mayar da dimokaradiyya wani makami na ci da ceto!

Daga karshe, idan har wadannan kasashen yammacin duniya na da burin aiwatar da dimokaradiyya mai inganci, ya zama wajibi su kiyaye, tare da martaba banbance banbance dake tsakanin kasashe, shiyyoyi, al’adu, da nau’o'in dimokaradiyya dake iya dacewa da al’ummu mabanbanta. Kaza lika ya zama wajibi su yi watsi da salon dimokaradiyyar yake yake.

Bugu da kari, lokaci ya yi da za su rungumi al’ummun duniya bisa tausayi da jin kai, wato dai su rungumi salon dimokaradiyyar al’umma, wadda za ta haifar da alfanu, da damar cin gajiya ga al’ummun kasashe musamman matalauta, ta yadda ba za a bar kowa a baya ba!