logo

HAUSA

Wadanda Suka Bijiro Da Batun "Halartar Taiwan A Taron WHA" Sun Ji Kunya!

2022-05-26 21:29:42 CMG HAUSA

Kasar Sin daya ce tak a duniya, kuma gwamnatin Jamhuriyar Jama’ar Kasar Sin, ita ce kadai halastacciyar gwamnati dake wakiltar kasar Sin. Haka kuma wanzuwar kasar Sin daya tilo a duniya, ita ce babbar manufar da kasashen duniya suka amince da ita, kana shi ne tushen siyasa na raya hulda tsakanin Sin da duk kasashen da suka kulla ko ma suke son kulla alaka da kasar Sin.

Duk da cewa kasar Amurka na daga cikin kasashen da suka amince da wannan manufa, baya ga sanarwoyi uku da kasashen biyu suka aminta da su a kan alakar dake tsakaninsu, amma a wasu lokuta ta kan yi biris tare da neman lalata tushen siyasa na huldar dake tsakaninta da kasar Sin, inda take ci gaba da hulda da yankin Taiwan na kasar Sin, har da neman sanya ta cikin tsarin hukumomin MDD, kamar babban taron majalisar kiwon lafiya ta duniya.

Sanin kowa ne cewa, Taiwan ba kasa ba ce, wani bangare ne na kasar Sin. Duk abun da wani kokari na jirkita gaskiya, ko kadan ba zai taba yin nasara ba, wato babban yanki da kuma yankin Taiwan duka suna karkashin ikon Jamhuriyar Jama’ar kasar Sin ne.

A kokarin tabbatar da gaskiya da kara martaba wannan manufa, babban taron majalisar kiwon lafiya na duniya karo na 75, ya yanke shawarar yin watsi da shawarar da kasashe daban-daban suka gabatar, na gayyatar Taiwan zuwa taron majalisar a matsayin ’yar kallo, matakin da masu sharhi ke nunawa karara cewa, manufar kasar Sin daya tilo a duniya, ita ce tsarin da al'ummomin kasa da kasa suka aminta da shi, kuma ba za a iya kalubalantarsa ba. Kuma wadanda suka bijiro da batun "halartar Taiwan a taron" sun ji kunya!

Mahukuntan kasar Sin dai na kara fahimtar da kasashen duniya game da manufar kasar Sin daya tak a duniya, duk da cewa, wasu kasashe suna sani da haka, amma su kan rufe ido su saba wannan manufa don neman biyan wata bukata ta kashin kai da neman tayar da fita. Inda a sanarwar da aka fitar bayan kammala cikakken zaman karo na shida na kwamitin tsakiya na JKS karo na 19, ta bayyana karara cewa, kasar Sin za ta ci gaba da martaba ka'idar kasancewar kasar Sin daya tak a duniya, da kuma matsaya irin wannan da aka cimma a shekarar 1992, wadda ke adawa da ayyukan ’yan aware dake neman ’yancin kai na Taiwan, da tsoma baki daga waje.

Wannan ya kara fayyace tsayin daka na kasar Sin, da kuma matsayinta na kare ikon mallakar kasa da cikakken yankunanta, har ma da tsaro da moriyar ci gabanta baki daya. Ta kuma sha alwashin dakile duk wani kutsen makiya daga waje da nufin kawo mata baraka a cikin gida. (Ibrahim Yaya)