logo

HAUSA

Gwamnatin Gambiya ta shirya hukunta tsohon shugaban kasar Jammeh

2022-05-26 11:20:31 CMG Hausa

A jiya Laraba gwamnatin kasar Gambia ta sanar cewa, ta shirya yanke hukunci kan tsohon shugaban kasar Yahya Jammeh, bisa zarginsa da hannu wajen salwantar rayuka sama da 240, da kuma muzgunawa ’yan kasar marasa galihu, har ma da wasu ’yan kasashen waje, a lokacin wa’adin mulkinsa tsakanin watan Julin shekarar 1994 zuwa Janairun 2017.

Babban atoni, kana ministan shari’a na kasar, Dawda Jallow, ya gabatar da takardar bayanai mai dauke da tuhume-tuhume 265 da ake yiwa tsohon shugaban kasar, inda ya gabatar da rahoton ga hukumar sulhu da bin diddigin hakkokin al’umma ta kasar wato (TRRC), wacce ta shafe sama da shekaru 20 tana gudanar da bincike game da kashe-kashen da ake zargin ko dai an aikata a lokacin mulkin Jammeh ko kuma yana da masaniyar aikata laifukan.

A cewar ministan, gwamnatin kasar ta amince da dukkan shawarwarin da hukumar TRRC ta gabatar game da neman zartar da hukuncin, inda ta nemi a hukunta tsohon shugaban kasar Gambiyan Yahya Jammeh, saboda tarin laifukan da ake zargin aikatawa tsakanin shekarun 1994 zuwa 2017, ministan shari’ar ya bayyana hakan ne a lokacin gabatar da rahoton takardar bayanan, wanda ya samu halartar mutanen da lamarin ya rutsa da su da iyalansu, da kungiyoyin fararen hula, da jami’an diflomasiyyar kasashen duniya dake kasar, ciki har da na MDD. (Ahmad)