logo

HAUSA

CBN ya kara kudin ruwa zuwa kaso 13 cikin dari

2022-05-25 10:28:41 CMG Hausa

Babban bankin Najeriya CBN, ya kara kudin ruwa da bankunan kasuwancin kasar ke karba kan basussuka zuwa kaso 13 bisa dari, karin da shi ne na farko da babban bankin ya yi cikin sama da shekaru 2 da suka gabata.

Da yake yiwa ’yan jarida karin haske game da hakan a jiya Talata, bayan kammala taron kwamitin tsara manufofin kudi a birnin Abuja, fadar mulkin kasar, gwamnan babban bankin Godwin Emefiele, ya ce an kara maki 150 kan kudin ruwan da bankuna suke caza ne, da nufin dakile hauhawar farashin kayan masarufi da Najeriya ke fama da shi.

Mr. Emefiele ya kara da cewa, CBN ya nazarci hanyoyin shawo kan wannan kalubale da dama, amma daga karshe ya yanke shawarar shawo kan matsin hauhawar farashin kayayyakin hade da bunkasar tattalin arzikin kasar tare.

Daga nan sai ya yi kira ga gwamnatin Najeriya da ta kara kwazo, wajen samar da karin kyakkyawan yanayin da zai ingiza ci gaban tattalin arzikin kasar yadda ya kamata.  (Saminu)