logo

HAUSA

’Yan bindiga sun kashe mutane 12 a arewa maso gabashin Nijeriya

2022-05-25 10:29:29 CMG Hausa

Rundunar ’yan sandan Nijeriya ta ce, wani gungun ’yan bindiga ya kaddamar da hari kan wani kauye a jihar Katsina dake arewa maso yammacin kasar, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutane 12 da jikkatar wasu da dama.

Kakakin rundunar ta jihar Katsina, Gambo Isa, ya shaidawa manema labarai cewa, ’yan bindigar da ake kira ’yan fashin daji sun farwa kauyen Gakurdi dake yankin karamar hukumar Jibia ne da safiyar jiya Talata.

A cewarsa, sun shiga kauyen ne a kan Babura 4, suna harbin kan mai uwa dawabi, lamarin da ya haifar da tashin hankali a kauyen tare da sanya mazauna gudun neman tsira. Yana mai cewa dukkan mutanen da aka kashe, an harbe su ne yayin da suke gonakinsu dake wajen kauyen. (Fa’iza Mustapha)