logo

HAUSA

Bankin raya Afrika ya bude taronsa na shekara a Ghana

2022-05-25 11:23:02 CMG Hausa

A jiya Talata, bankin raya ci gaban Afrika (AfDB), ya bude taronsa na shekarar 2022 a Accra, babban birnin kasar Ghana, wanda ya samu halartar muhimman mutane, da ’yan siyasa, da kwararrun masana harkokin mulki daga kasashen Afrika.

A jawabinsa na bude taron, shugaban kasar Ghana, Nana Addo Dankwa Akufo-Addo, ya bukaci bankin raya nahiyar da ya taimakawa Afrika, wajen ankarar da nahiyar game da yadda za a kaucewa barnata kudade ba bisa ka’ida ba, a cikin ajandar bankin na yin sauye-sauye.

Shugaban bankin na AfDB, Akinwumi Adesina, ya ce bankin, da kuma hukumar gudanarwar kungiyar tarayyar Afrika, sun kafa wani shirin samar da abinci na gaggawa, domin magance matsalar karancin abinci dake yiwa nahiyar barazana a sakamakon barkewar yaki a tsakanin kasashen Rasha da Ukraine. (Ahmad)