logo

HAUSA

Wani kamfanin kasar Sin ya kaddamar da gidauniyar tallafawa al’umma a kasar Saliyo

2022-05-25 10:45:57 CMG Hausa

Kamfanin “Leone Rock Metal Group” na kasar Sin, mai aikin hakar ma’adanai a kasar Saliyo, ya sanar da kaddamar da gidauniyar bunkasa ci gaban al’ummar kasar.

Kamfanin ya ce zai rika kebe kaso daya bisa dari na ribar da yake samu a duk shekara, wajen tallafawa al’ummun gundumar Tonkolili, dake lardin arewacin kasar inda yake gudanar da ayyukansa.

Da yake karin haske game da hakan yayin kaddamar da gidauniyar, babban jami’in kamfanin Zhao Ting, ya ce har kullum kamfaninsa a shirye yake, da ya ba da gudummawa ga manufar raya masana’antun kasar Saliyo, tare da bunkasa rayuwar mazauna wuraren da yake gudanar da ayyukansa.

A nasa bangare, shugaban kasar Saliyo Julius Maada Bio, ya bayyana matakin da kamfanin ya dauka a matsayin mai matukar muhimmanci, a fannin bunkasa yankin da yake gudanar da ayyukan sa.  (Saminu)