logo

HAUSA

Rayuka nawa za a kashe kafin 'yan siyasar Amurka su farga?

2022-05-25 20:11:04 CMG Hausa

Jiya ne, agogon wurin, aka kai wani mummunan hari a wata makarantar firamare da ke jihar Texas ta Amurka, inda aka kashe sama da mutane 20, ciki har da yara a kalla 19. Wannan danyen aiki ya samo asali ne kan yadda ‘yan siyasar Amurka ba sa mutunta ‘yancin jama’a. Harin da aka kai makarantar firamaren, yana zuwa ne a daidai lokacin da shugabannin Amurka ke shagaltuwa wajen neman kafa rukunonin yin fito na fito a nahiyar Asiya. Wannan na nuna cewa, miliyoyin rayukan da aka yi hasara sanadiyar sabon nau’in annobar COVID-19 ba komai ba ne a wajen ’yan siyasar Amurka, kuma jinin da aka zubar sanadiyar harbin shi ma ba komai ba ne, abu mafi muhimmanci a gare su kawai, su ne son kai na siyasa da mulkin danniya na Amurka. (Ibrahim)