logo

HAUSA

Jami’i ya ce yakin Rasha da Ukraine yana dakile bunkasar tattalin arzikin Afrika

2022-05-25 11:24:51 CMG Hausa

Wani jami’in MDD ya bayyana cewa, rikicin Ukraine da Rasha yana haifar da mummunan tasiri, wanda ke shafar bunkasar tattalin arzikin Afrika.

Walid Badawi, babban jami’in shirin bunkasa ci gaba na MDD (UNDP), dake kasar Kenya ya ce, yakin ya yi sanadiyyar tashin farashin muhimman kayayyakin bukatun yau da kullum a nahiyar.

Jami’in MDDr ya bayyana cewa, rikicin ya haifar da sauya akalar muhimman ayyukan tallafin raya ci gaba daga Afrika zuwa kasashen da yakin ya shafa. (Ahmad)