Abubakar Sulaiman Gezawa: Ina kira ga matasan Najeriya da su kara rungumar karatu don bautawa kasarsu
2022-05-24 15:06:28 CMG Hausa
Abubakar Sulaiman Gezawa, dan Najeriya ne wanda a yanzu haka yake karatu a jami’ar Xiamen dake kudancin kasar Sin, kuma a kwanan nan ya yi nasarar gama karatun digiri na uku.
A yayin zantawarsa da Murtala Zhang, Abubakar Gezawa, wanda ya dade yana karatu da zama a birane daban-daban na kasar Sin, ya bayyana fahimtarsa game da halayen mutanen kasar, gami da al’adunsu masu ban sha’awa. Kana, ya bayyana ra’ayinsa kan bambancin yanayin karatu tsakanin gida Najeriya da kasar Sin, da kuma kiransa ga matasan Najeriya. (Murtala Zhang)