logo

HAUSA

Masu goyon bayan halartar Taiwan taron WHA sun ji kunya

2022-05-24 19:20:48 CMG Hausa

Babban taron majalisar kiwon lafiya na duniya karo na 75, ya yanke shawarar kin shigar da abin da aka kira "gayyatar Taiwan don halartar taron majalisar a matsayin mai sa ido" da wasu kasashe suka gabatar a cikin ajandar taron. Wannan ita ce shekara ta 6 a jere da majalisar ta WHA ta yi watsi da shawarwarin da suka shafi yankin Taiwan, lamarin da ke nunawa karara cewa, manufar kasar Sin daya tilo a duniya, ita ce manufar da al'ummar duniya baki daya suka amince da ita, kuma ba za a iya kalubalantarta ba. Wadanda suka bijiro da batun "halartar Taiwan a taron" sun ji kunya!

Makusudin gabatar da wannan magudi na siyasantar da batutuwan da suka shafi kiwon lafiya tare da dakushe muradun lafiyar jama'a na kasa da kasa shi ne, neman yin "amfani da Taiwan don sarrafa kasar Sin". “Masu neman ‘yancin kai na Taiwan” suna fakewa da makiya daga waje da kuma amfani da annoba, wajen neman 'yancin kai. Amma lamarin ya zama cewa, wannan mafarki ne kawai. (Ibrahim)