logo

HAUSA

GDPn Najerya ya karu da kashi 3.11 a rubu’in farkon bana duk da raguwar kudin mai

2022-05-24 11:08:51 CMG Hausa

Hukumar kididdiga ta kasar Najeriya NBS ta ce, alkaluman tattalin arzikin GDPn Najeriya ya karu da kashi 3.11 bisa 100 a rubu’in farko na shekarar 2022, idan an kwatanta da na makamancin lokacin bara, duk da raguwar kudaden da kasar ke samu daga albarkatun man fetur a makamancin lokacin.

Adadin karuwar da aka samu ya karu da sama da kashi 0.51 bisa 100 a rubu’in farko na shekarar 2021, sai dai ya ragu da kashi 3.98 bisa 100 wanda aka samu a rubu’i na hudu na shekarar 2021, kamar yadda sabon rahoton na NBS kan tattalin arzikin kasar ya nuna.

A cewar NBS, wannan karuwar da aka samu ya nuna cewa, an samu dorewar bunkasuwar tattalin arikin kasar a cikin rubu’i shida a jere tun bayan karayar tattalin arzikin da kasar ta fuskanta a shekarar 2020, inda a wancan lokacin aka samu raguwar GDPn a rubu’i na biyu da na uku a shekarar 2020.

Alkaluman na NBS ya nuna cewa, a lokacin da kasar ta fuskanci koma bayan bunkasar tattalin arzikin, ayyukan hako albarkatun mai wanda shi ne jigon tattalin arzikin Najeriya, ya samu koma baya a rubu’i da dama da suka gabata. (Ahmad)