logo

HAUSA

Jakadan Sin ya bukaci kasa da kasa su taimakawa inganta tsaron Somaliya da ayyukan jin kan bil Adama

2022-05-24 11:07:16 CMG Hausa

Wakilin kasar Sin ya bukaci kasa da kasa su tallafa don inganta sha’anin tsaron kasar Somaliya da kuma yanayin ayyukan jinkai a yayin da kasar ta kammala zaben shugaban kasa da na ’yan majalisun dokokinta.

A makon jiya, an yi nasarar kammala zaben shugaban kasar, inda aka bude sabon shafi a tsarin shugabancin Somaliya. Halin da ake ciki a yanzu mai matukar wahala ne. Kasar Sin na fatan kafa sabuwar gwamnatin Somaliyan, zai samar da kyakkyawan tsammanin cewa, Somaliya za ta yi amfani da wannan damar wajen gaggauta gina kasa da kuma cimma nasarar dorewar zaman lafiya da tsaro ba tare da bata lokaci ba, a cewar Dai Bing, mataimakin zaunannen wakilin kasar Sin a MDD.

Har yanzu batun zaman lafiya da tsaro a Somaliya yana matukar fuskantar kalubaloli. Babban abin da zai taimaka wajen sauke muhimmin nauyin tabbatar da tsaro a kasar shi ne aiwatar da dabarun wanzar da tsaro da aka tsara, da gaggauta kafa rundunar dakarun wanzar da tsaro mai karfin gaske, kuma a yi kokarin inganta yanayin tsaron kasar yadda ya kamata. Dai ya bayyana hakan ne ga taron kwamitin sulhun MDD kan batun Somaliya. (Ahmad)