logo

HAUSA

Babban bankin kasar Ghana ya ayyana karin kudin ruwa domin dakile hauhawar farashin kayayyaki

2022-05-24 10:24:04 CMG Hausa

Babban bankin kasar Ghana, ya ayyana karin maki 200 na kudin ruwa kan basussuka da bankuna ke bayarwa, da nufin dakile hauhawar farashin kayayyaki da kasar ke fuskanta, a gabar da sassan duniya ke tunkarar rashin tabbas game da farashin hajoji, da sauyin yanayin samar da hajojin ga kasuwannin duniya.

A jiya Litinin ne gwamnan babban bankin kasar ta Ghana Ernest Addison, ya bayyana hakan, yayin taron manema labarai, bayan kammala taron kwamitin tsara manufofin kudin kasar MPC karo na 106.

Mr. Addison ya ce rashin damar shigar da karin albarkatu cikin harkar samar da abinci, da karin kudaden shigo da kayayyaki, na ci gaba da ingiza farashin albarkatun man fetur, da hauhawar farashin sufuri, da yiwuwar samun karin farashin harajin hadimomin yau da kullum a gidajen al’umma, da matsin da kudaden albashi ke fuskanta, bisa tashin gwauron zabin kayayyakin masarufi da ake tunkara a kasar.  (Saminu)