logo

HAUSA

Manyan biranen Ghana sun gamu da ambaliya sakamakon ruwan sama

2022-05-23 10:21:07 CMG Hausa

Wasu daga cikin manyan birane da garuruwan kasar Ghana sun gamu da ambaliyar ruwa a ranar Lahadi biyo bayan shafe sama da sa’o’i 12 ana sheka ruwan sama, lamarin da ya haifar da cikas a fannin sufurin ababen hawa a wasu yankunan kasar.

Manyan hanyoyin mota a Accra, babban birnin kasar Ghana, da kuma birnin Tema mai tashar ruwa dake gabashin kasar, na daga cikin biranen da aka fuskanci ambaliyar, lamarin da ya haifar da tsananin wahala ga masu ababen hawa wajen gaza bin hanyoyin, kana wasu da dama daga cikin matafiya sun makale.

Eric Adade, wani direban motar haya dan shekaru 48, wanda ya nufi birnin Accra daga garin Tema, a lokacin da lamarin ya faru, ala tilas ya ajiye motarsa a gefen titi sakamakon yadda ruwan ya malale hanyar, har ma ya kasa tantance wajen da zai bi.

Ya ce, “lamari ne mai matukar wahala mutum ya iya tuki a wannan yanayin ruwa, don haka na yanke shawarar ajiye motata, har sai an samu tsakaitawar al’amurra kafin na cigaba da tukin.” Ya ce “ba zan yi wasa da rayuwata ba."

A birnin Tema, tashoshin manyan motoci da kanana sun cika da fasinjoji wadanda suka makale, suna zumudin isa wuraren da suke son zuwa. (Ahmad)