logo

HAUSA

Ya dace kasashen dake yankin tekun Indiya da Fasifik su yi hattara game da tsarin IPEF na Amurka

2022-05-23 21:25:22 CMG Hausa

 Wani tsari da ake kira "hadin gwiwar yankunan dake tekun Indiya da Fasifik" na Amurka ya bayyana a hukumance. A yau ne, shugaban Amurka da ke ziyara a kasar Japan, ya sanar da kaddamar da hadin gwiwar tattalin arziki na kasashen dake tekun Indiya da Fasifik" (IPEF). Sai dai kuma, galibin wannan tsari ba shi da ma'ana kuma yana da rudani, baya ga ba da shawarar raba gari da kasar Sin a cikin tsarin samar da kayayyaki da kuma bayyana cewa, ba za a rage harajin shiga kasuwannin Amurka ba. Wasu manazarta na cewa, wannan dabara ce ta Amurka kawai ta "kasuwanci ba tare da saka jari ba". (Ibrahim)