Kamfanonin Amurka Sun Ci Riba Yayin Da Ake Fama Da Wahalar Hauhawar Farashin Abinci
2022-05-23 20:12:40 CMG Hausa
Abokaina, a wajenku, farashin kayayyakin abinci ya karu?
Yakin da ake yi tsakanin Rasha da Ukraine, da takunkuman da kasashen yamma suka kakabawa Rasha, sun dakatar da cinikin takin zamanin da ake samarwa a kasashen Rasha da Belarus, lamarin da ya sa kudin da ake kashewa a aikin gona ya karu. Baya ga wannan batu, yadda Ukraine da Rasha suka dakatar da aikin fitar da alkama da masara zuwa kasashen waje, sun sa farashin kayayyakin abinci na kasashe daban daban ya karu sosai. Yanzu a kasar Masar, farashin burodi ya karu da kashi 50%. Yayin da a kasar Lebanon, farashin burodi guda daya ya kai dalar Amurka 9. Sa’an nan a kasar Senegal, ko da yake gwamnati ta dauki matakan dakile hauhawar farashin kayayyaki, amma farashin burodi ya ci gaba da karuwa daga Cefa 150 zuwa Cefa 175, wato farashin ya karu da kashi 16.6%.
Hauhawar farashin abinci wahala ce ga jama’a, amma duk da haka, akwai wanda ya ci riba sakamakon wannan matsala. Mun san wasu shahaharrun manyan kamfanoni 4 suna shawo kan kashi 80% na cinikin hatsin kasa da kasa, sa’an nan kasar Amurka ta mallaki 3 daga cikinsu, wato kamfanonin ADM, Bunge, da Cargill. Wadannan kamfanoni sun ci riba sosai bisa hauhawar farashin abincin da ake samu, inda kudin shigarsu ya karu da kashi 53%, 80%, da 64%.
Yakin da Rasha da Ukraine suke yi ya sa dukkan kamfanonin hatsi da na samar da makamai na kasar Amurka cin riba sosai. Saboda haka, ba abin mamaki ba ne yadda kasar Amurka ba ta son ganin karshen yakin, inda ta yi ta jigilar makamai zuwa Ukraine don tabbatar da samun daidaituwa tsakanin karfin sojin kasashen 2, tare da tsai da kudurin “ yaki da kasar Rasha, har sai dukkan ‘yan kasar Ukraine sun mutu”.
Hakika su ma manyan kamfanonin cinikin hatsi na kasar Amurka sun dade suna korafe-korafe kan cewar, farashin kayayyakin abincin duniya bai yi tsada ba. Saboda haka sun yi ta matsawa gwamnatin kasar Amurka lamba, don neman habaka yin amfani da makamashin da aka samar daga hatsi. Zuwa shekarar 2021, hatsin da kasar Amurka ta sarrafa shi zuwa makamashi ya kai ton miliyan 170, wanda ya kai kashi 40% na dukkan hatsin da aka yi amfani da shi a kasar. Wadannan hatsi, idan an raba su ga al’ummomin duniya, za a iya ciyar da mutane miliyan 460 har tsawon shekara guda. Sai dai kasar Amurka ta kone su kawai a matsayin makamashi. Tunanin kamfanonin kasar Amurka shi ne: Idan akwai dimbin hatsin da zai sanya dukkan mutanen duniya su ci su koshi, to, a kone wasunsu a matsayin makamashi, har lokacin da wasu mutane sun fara fama da yunwa, ta yadda ake son daga farashin hatsin. Wato kamfanonin ba za su so a sayar da hatsi a matsayin abinci ba, illa dai farashinsa ya karu zuwa wani matsayin da zai gamsar da su ba. Ribar da kamfanonin Amurka suke samu na dogaro ne kan dimbin mutanen da suke fama da yunwa a sauran kasashe.
Ta haka za mu iya fahimtar cewa, moriyar kasar Amurka ta kan saba wa moriyar mutanen duniya: Idan ana fama da tashin hankali a sauran kasashe, kana mutanen kasashen suna shan wahala, to, kamfanonin kasar Amurka za su ci riba sosai, kana tattalin arizkin kasar ma zai karu cikin sauri. Idan farashin abinci ya karu, kasar Amurka za ta iya sayar da hatsi don cin riba. Idan akwai matsalar karancin makamashi, kasar za ta sayar da man fetur don samun kudi. Idan ana yaki, to, sai ta sayar da makamai don neman riba. Idan wata kasa ta gamu da matsalar tattalin arizki, a kan janye kudin jari daga wannan kasa. Sa’an nan wadannan jari ma su kan shiga cikin kasar Amurka, wadanda suke wadatar da mutanen kasar. Wannan batu, a ganina, shi ne dalilin da ya sa kasar Amurka ke kokarin ta da zaune-tsaye da rikici a wurare daban daban na duniya. (Bello Wang)