logo

HAUSA

Mutane 35 sun mutu a harin da aka kai wani sansanin soji a Burkinafaso

2022-05-22 15:31:26 CMG Hausa

Rahoton da kamfanin AFP na kasar Faransa ya gabatar ya bayyana cewa, hukumar sojin kasar Burkinafaso ta bayyana a cikin wata sanarwar da ta fitar cewa, jiya Asabar 21 ga wata da safe, an kai wa rundunar sojojin kasar dake yankin Bourzanga hari, inda sojoji suka harbe ‘yan ta’adda a kalla 30 har lahira, kana sojoji biyar sun rasa rayukansu.

Hukumar sojin kasar ta yi tsokaci cewa, sojojin yankin sun mayar da martani da karfi ga harin da ‘yan ta’adda suka kai wa sansaninsu.

Tun bayan shekarar 2015, kasar Burkinafaso ke fama da hare-haren ‘yan bindiga, inda mutane sama da 1000 suka rasa rayukansu, yayin da wasu miliyan daya sun rabu da muhallansu. (Jamila)