logo

HAUSA

Masanin Najeriya: Yadda Amurka da kasashen yamma ke furta kalaman tsokana zai kara rashin zaman lafiyar duniya

2022-05-22 17:51:27 CMG Hausa

Wani masanin kasar Najeriya, Joseph Peter Ochogwu, ya bayyana a yayin hira da ‘yan jarida cewa, Amurka da kungiyar NATO, suna cigaba da neman tada jijiyar wuya, da yin fito-na-fito, da bayyana kalaman tsokana, game da rikincin Rasha da Ukraine. Lamarin da ke kara ta’azzara karuwar rashin zaman lafiya.

Joseph Peter Ochogwu, farfesa ne a jami’ar Nile dake Najeriya, yace, NATO da kawayenta, suna kara haifar da tashin rikici, sannan tsadar farashin muhimmin kayan masarufi a duniya yana kara kamari, wanda hakan kadai yana iya yin sanadiyyar rashin zaman lafiya a sauye-sauyen fagen siyasar duniya.

Ochogwu ya bayyana farin cikinsa game da matsayar da kasar Sin ta dauka, wajen kokarin jan hankali don samun zaman lafiya, da kokarinta na daga matsayin neman hawa teburin tattaunawar sulhu game da rikicin tsakanin Rasha da Ukraine. Ya bayyana cewa, kasar Sin, ba kamar kasar Amurka da sauran kasashe ba ne, wadanda ke yin kiraye-kirayen neman kakaba takunkumai, maimamon hakan, Sin ta zabi yin aiki tukuru, wajen neman maslaha don warware rikicin ta hanyar bin matakan siyasa kan batutuwan dake shafar rikicin Rasha da Ukraine. A bayyane take cewa, kasar Sin ta yanke shawara ba tare da dogaro kan kowa ba, game da matakan diflomasiyyarta.(Ahmad)