logo

HAUSA

Sharhi: Kafofi na wai masu ‘Yanci

2022-05-22 22:21:28 CMG Hausa

Kwanan nan, ministan watsa labarai da raya al’adu na Najeriya Lai Mohammed, ya ja kunnen kamfanoni mamallaka dandalolin sada zumunta, da su daina baiwa kungiyar nan ta IPOB, ta ‘yan aware dake kudancin Najeriya, damar yada bayanai na rura wutar rikici, da kabilanci a kan shafukan su.

Lai Mohammed ya yi wannan gargadi ne a yayin wata tattaunawa da tawagar kamfanin Facebook. Ya kara da cewa, gwamnatin Najeriya za ta sanya ido sosai kan shafukan Facebook, da sauran dandaloli makamantan sa a kwanaki masu zuwa, domin tabbatar da ko facebook din ya kiyaye wannan jan hankali, yayin da kasar ke kara azamar yayata manufar amfani da dandalolin sada zumunta ta hanyoyin da suka kamata.

A cewar sa, an riga an ayyana kungiyar IPOB a matsayin ta ‘yan ta’adda, don haka babu wani dalili da zai sa Facebook ya rika baiwa kungiyar damar shiryawa, ko gabatar da farfagandar kiyayya, ko wargaza zaman lafiyar Najeriya.

Idan ba a manta ba, a bara, gwamnatin Nijeriya ta dakatar da ayyukan shafin sada zumunta na Twitter a fadin kasar,  sakamakon yadda kafar Twitter ya goge wani sakon da shugaban Nijeriya Mohammadu Buhari ya wallafa ta kafar, inda ya gargadi masu tada rikici a kasar. Bayan da Twitter ya goge sakon shugaba Buhari, ministan yada labarai da raya al’adu na kasar Lai Mohammed ya zargi Twitter da nuna fuska biyu, bisa ga yadda ya goge sakon shugaban, amma ba tare da daukar wani mataki kan sakonnin da jagororin ‘yan aware a Nijeriya suke wallafawa ba. Ya kara da cewa, a lokacin da mutane suke kona ofisoshin ‘yan sanda tare da kashe su yayin zanga-zangar End SARS, a ganin Twitter, suna da ‘yancin gudanar da zanga-zanga. Amma a lokacin da makamancin lamarin ya faru a Amurka, sai ya zama tawaye.

Sai dai hakan ba kawai ke faruwa a Nijeriya ba. Yayin da aka samu matsalar gyara doka a yankin Hong Kong a shekarar 2019, shahararrun kafofin sada zumunta na kasar Amurka kamar su Twitter da Facebook da sauransu sun taba dakatar da shafukan masu amfani da kafar sama da dubu daya bisa dalilin wai suna ba da labaran karya ko suna samun goyon bayan gwamnatin kasar Sin, amma hakika kafofin sun gabatar da labarai na hakika da suka faru a yankin Hong Kong. A sa’i daya kuma, kafar Twitter ba ta kula da sakwannin da suke shafa wa ‘yan sandan Hong Kong da gwamnatin kasar Sin bakin fenti ba.

Irin wannan abubuwa ba sa lisaftuwa. Matsayin da kafofi irnsu Facebook da Twitter suka dauka ya dogara ne ga rukunonin da ke mara mata baya, kuma moriyar kasar Amurka ce kafofin ke wa aiki, a maimakon a ce su kamfani masu zaman kansa. A kasashen Afghanistan da Iraki da Syria da Libya da sauransu, Amurka ta yi ta tada zaune tsaye da mara wa masu adawa da gwamnati baya, don cin moriyarta, kuma kafofinta na yanar gizo ma suna ba da taimako.(Mai Zane:Mustapha Bulama)