logo

HAUSA

Auren mata ta gari ko namiji na gari yana tsawaita rayuwar namiji ko mace

2022-05-22 15:29:28 CMG Hausa

 

Wani rahoton da gwamnatin kasar Birtaniya ta kaddamar a kwanan baya ya nuna cewa, a zahiri auren mata ta gari ko namiji na gari yana tsawaita rayuwar namiji ko mace.

Hukumar kididdiga ta kasar Birtaniya ta bayyana cewa, masu nazari sun tantance mutuwar mutane ‘yan shekaru sama da 20 da haihuwa miliyan 5 baligai daga Ingila da Wales wadanda suka mutu daga shekarar 2010 zuwa 2019. Sun gano cewa, yawan mutuwar wadanda ba su yi aure ba ya fi wadanda suka yi aure yawa har sau daya. Karo na farko kenan da hukumar ta gudanar da irin wannan nazari.

Masu nazarin sun raba wadannan mutane zuwa rukunoni guda 2, wato ‘yan shekaru 20 zuwa 64 da haihuwa da kuma ‘yan shekaru sama da 65 da haihuwa. Dukkansu sun nuna cewa, yawan mutuwar wadanda suka yi aure ba shi da yawa.

A cikin ‘yan shekaru 20 zuwa 64 da haihuwa, yawan mutuwar mazan da ba su yi aure ba ya fi ta mazan da suka yi aure yawa har sau 3. Kana kuma yawan mutuwar matan da ba su yi aure ba ya fi ta matan da suka yi aure yawa har sau 2.3.

A cikin ‘yan shekaru sama da 65 da haihuwa, yawan mutuwar wadanda suka yi aure ba shi da yawa.

Wani jami’in kula da alkaluman kididdigar yawan mutuwa na hukumar kididdigar kasar Birtaniya ya yi karin bayani da cewa, karo na farko kenan da gwamnatin kasar Birtaniya ta yi nazari kan yawan mutuwar al’ummar kasar bisa halin da ake ciki a kasar ta fannin aure. Bayan da aka yi nazari kan alkaluman na tsawon shekaru 10, an gano cewa, yawan mutuwar maza da mata wadanda suka yi aure ko kuma suke da masoyiyya ko masoyi ya fi karanci, in an kwatanta su da wadanda ba su yi aure ba, ko sun kashe aure ko kuma matarsa ko mijinta ya riga mu gidan gaskiya.

Alkaluman da aka samu a wannan karo sun tabbatar da sakamakon da aka samu cikin nazarce-nazarcen da aka gudanar a baya, wato wadanda suka yi aure sun fi samun tsawon rayuwa, sun fi ji dadin zaman rayuwarsu, sun kuma fi kasancewa cikin koshin lafiya.

Dangane da lamarin, madam Zhang Chuji, wata likita ce da ke aiki a asibitin Tiantan na Beijing ta yi nuni da cewa, dalilin da ya sa haka shi ne domin masoyi da masoyiyya suna kulawa da juna sosai, suna bukatar juna wajen binciken lafiya a lokacin gano kamuwa da cuta ko akwai alamar kamuwa da cuta. Haka kuma farin ciki yana amfanawa lafiya da sassauta matsin lambar da ake fuskanta, da kuma kara azama kan rayuwa ta hanyar da ta dace. Har ila yau idan an mai da hankali kan iyali, to, za a kaucewa yin abubuwa masu hadari. (Tasallah Yuan)