logo

HAUSA

Sojojin Najeriya sun kashe 'yan bindiga biyu a kudancin Najeriya

2022-05-22 17:49:38 CMG Hausa

Rundunar sojojin Najeriya ta sanar a ranar Asabar cewa, ta kashe wasu ‘yan bindiga biyu wadanda aka bayyana a matsayin mayakan ‘yan aware na Biafra (IPOB), da na kungiyar Eastern Security Network a jahar Imo dake kudancin Najeriya.

Cikin wata sanarwa, Onyema Nwachukwu, kakakin rundunar sojojin Najeriya, ya bayyana cewa, dakarun sojojin sun yi nasarar fatattakar ‘yan bindigar ne a wani sansanin horaswa na mayakan dake wani kauye a karamar hukumar Orlu a jahar, kafin daga bisani suka samu nasarar kashe su a yayin fafatawar.

Nwachukwu ya ce, sansanin ba da horon mallakin kungiyar IPOB ne, kuma a wajen ne ake shirya hare-haren ta’addanci daban-daban da ake kaddamarwa a wasu daga cikin jahohin kudancin kasar.

A cewarsa, sojojin sun kuma lalata cibiyoyin bada horo da sauran kayayyakin da mayakan ‘yan awaren ke amfani da su, da suka hada da wani dakin taro da kuma ma’aikatar kera makamai.(Ahmad)