logo

HAUSA

Zhang Na: Ina kokarin zama idanun abokai makafi don taimaka musu wajen karanta litattafai

2022-05-21 20:22:47 CRI

Zhang Na, mai shekaru 42 da haihuwa, an haife ta ne a karkarar gundumar Dongguang, na lardin Hebei dake arewacin kasar Sin, saboda nakasar gani ta haihuwa, ba ta iya gani sosai. Lokacin da take karama, ba ta iya wasa da sauran yara yadda ya kamata, don haka ta kan boye a cikin gida ita kadai.

Bayan ta shiga makaranta, ko ta zauna a sahun farko na ajin, ba ta iya ganin abubuwan da aka rubuta a allo. Zhang Na ta ce, abin da ya burge ta shi ne, abokin karatu dake amfani da tebur daya da ita ya kan taimaka mata wajen karanta rubutun, malamai kuma su kan kara sauti da gangan, ko kuma rage saurin magana yayin koyarwa. Amma duk da haka, ta kan kasa fahimtar yawancin abubuwan da malamai suke koyar musu.

Zhang Na ta ce, a lokacin tana cike da rashin imani sosai, ta yi kuka ta tambayi mamarta cewa, “Me ya sa bana iya gani?” A wannan lokacin, mamarta ta sai dai ta yi shiru kawai, ta kuma fita waje don ya yi kuka a asirce.

Domin ba da dama ga Zhang Na ta ci gaba da bin yunkurin karatun makarantar, mamarta ‘yar karkara, wadda ba ta taba zuwa makaranta ba, ta fara karatu tare da Zhang Na. Zhang Na ta ce, kullum sai mamarta ta koya wa kanta, sannan ta koya mata.

Zhang Na ta tuna cewa, a cikin shekarun 1980, an sha samun katsewar wutar lantarki a yankunan karkarar wurinsu, da dare, tana yin karatu da mahaifiyarta a karkashin fitila mai amfani da kananzir. Domin ba ta iya gani sosai, Zhang Na tana bukatar ta kasance kusa da littafin sa’ad da take karantawa, don haka fitulun kananzir su kan kone gashinta.

Bugu da kari, saboda kasa gani sosai, ta kan kashe lokuta da yawa fiye da sauran dalibai a lokacin jarrabawa, don haka, a farko kullum ba ta iya kammala jarrabawa cikin lokaci.

Amma Zhang Na ta ki amincewa da shan kaye, ko yaushe tana amfani da lokaci da yawa fiye da abokan karatunta, a karshe dai, ta kai matsayin gaba a ajinsu a fannin karatu. Zhang Na ta ce, a lokacin ta yi imani da gaske cewa, abin da sauran dalibai za su iya yi, ita ma za ta iya yi da kyau.

Ko da yake bayan kammala karatunta a sakandare, Zhang Na ba ta ci gaba zuwa jami’a ba. Amma ba ta daina karatun ta ba, kuma ta dage da karatu a kowace rana, ta hanyar amfani da na’urar taimakawa ganin abubuwa.

Zhang Na tana son yin rubutu, a lokacin da ta fara aiki, ta rubuta wata kasida game da gogewar rayuwarta, ta kuma mika wa wani gidan rediyo na wurinsu. Bayan 'yan kwanaki, an watsa labarin. Masu saurare da yawa sun rubuta mata wasika, inda suke karfafa mata gwiwa wajen cimma burinta.

Domin rama nadama na kasa zuwa jami'a, Zhang Na ta fara karatun kwasa-kwasan jami'a da kanta. Bayan shekaru 3 na aiki tukuru, ta sami takardar shaidar difloma. Daga baya kuma ta yi amfani da shekaru 3 domin samu digiri na farko. Bugu da kari, ta kuma koyi fasahar kwamfuta, yanzu ba kawai tana iya bugawa da sauri ba, har ma tana iya sarrafa wasu manhajoji kamar ofis, hoto, sarrafa sauti da bidiyo yadda ya kamata.

Zhang Na tana kara jin dadi, a ganinta, ya kamata ta raba farin cikin da take ji sakamakon karatu, tare da wadanda ke cikin hali irin daya da nata, wato wadanda ke fuskantar matsalar gani.

A shekarar 2013, Zhang Na ta fito da wani tunani, na yin amfani da yanar gizo don karanta litattafai ga makafi, wanda hakan zai sama musu damar iya samun ilmi cikin sauki, da samu kwarin gwiwa kan zaman rayuwarsu.

Don haka, Zhang Na ta sayi kwamfutoci da na'urorin yin rikodin a watan Nuwamba na shekarar 2014, ta kuma bude shafinta na musamman a dandalin sada zumunta.

A farko, Zhang Na ita kadai take yin dukkan ayyuka, kamar su dauka murya, da sanya kide-kide, da kuma loda shiri a yanar gizo. Saboda saurin ganin ta ba ya dacewa da saurin karatu, shi yasa take karanta ko wane labari sosai kafin ta fara yin rikodin. Duk da haka, ta kan karanta ba daidai ba, don haka dole ne ta maimaita akai-akai. Don haka, tana bukatar lokuta masu yawa don gama wani labari mai tsawon ‘yan mintoci kadan.

Ko da yake wannan aikin ya sa Zhang Na ta sha wahala sosai, amma ba ta gajiya da shi. Ta yi imani cewa, matsaloli suna da iyaka amma kauna ba ta da iyaka. Abubuwan da take yi suna da ma’ana idan dai suna taimakawa masu bukata su sami jin dadin karatun.

Baya ga haka, Zhang Na tana karfafa gwiwar masu karatu su ma su rubuta, da karanta abubuwa, da kuma aikawa a shafinta na dandalin sada zumunta. Da haka wasu nakasassun gani kamar ta, sannu a hankali suka juya matsayinsu daga masu sauraro zuwa mahalarta.

Zhang Na ta gaya mana cewa, "Yanzu akwai masu aikin sa kai na karatu fiye da 50 da suka fito daga biranen Beijing, da Shanghai, da lardunan Hebei, da Sichuan da sauran wurare. Ba mu taba sanin juna ba har sai da muka zama abokai saboda littafi, kuma sau da yawa muna gaya wa juna abubuwan da muke ji kan karanta litattafai.”

Tun bayan bude wannan shafin a dandalin sada zumunci, har zuwa yanzu, an fitar da ayyukan sauti sama da 1,400, tare da samu masu sauraro kusan 2,000. Zhang Na tana kara kokarinta kan wannan aiki, a cewarta, "Ba ni da kyakkyawar murya ko karewar karatu, amma ina da zuciya mai zafi, shirye nake in samar da haske ga masu kaunar karatu, wadanda ke fuskantar matsala a fannin."