logo

HAUSA

Gwamnatin Nijeriya za ta sanya mutane miliyan 83 cikin shirin inshorar lafiya

2022-05-21 16:58:28 CRI

Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari, ya ce akalla al’ummar kasar miliyan 83 masu fama da talauci, za su shiga cikin tsarin inshorar lafiya na kasar, a wani yunkuri na ganin tsarin ya kunshi kowa.

Muhammadu Buhari ya bayyana haka ne a Abuja babban birnin Kasar, yayin da yake rattaba hannu kan dokar inshorar lafiya ta 2022 da aka zartar a bayan nan.  

A cewarsa, za a kafa wani asusu da zai tabbatar da amfanawa mutane miliyan 83 da ba za su iya biyan kudin inshorar da ake bukata ba.

Ya kara da cewa, hukumar kula da inshorar lafiya ta kasar (NHIA), za ta hada hannu da tsarukan inshorar lafiya dake karkashin gwamnatocin jihohi domin amincewa cibiyoyin kiwon lafiya amfani da tsarin da shigar da al’ummar kasar cikinsa da nufin tabbatar da samar da ingantaccen kiwon lafiya.

Sabuwar dokar za kuma ta ba hukumar NHIA da gwamnatocin jihohi damar samar da tsarin kula da bayanai da amfani da na’urori domin kyautata aikin tattara bayanan da bibbiya da tabbatar da ingancin aikin. (Fa’iza Mustapha)