logo

HAUSA

An dage ranar dawo da zirga-ziragr jirgin kasan tsakanin Abuja da Kaduna

2022-05-21 21:00:09 CMG Hausa

Hukumar kula da sufurin jiragen kasa ta Nijeriya, ta sanar da dage komawar zirga-zirgar jirgin kasa tsakanin babban birnin kasar Abuja da kuma Kaduna dake arewacin kasar, wanda aka dakatar bayan harin da aka kai masa a cikin watan Maris.

A farkon mako ne hukumar ta sanar da cewa jirgin kasan zai dawo da zirga zirga tsakanin biranen biyu a ranar 23 ga wata.

Wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wane ne ba, suka kai wa jirgin da ya fito daga Abuja akan hanyarsa ta Kaduna hari a garin Rijana na Kaduna, lamarin da ya yi sanadin mutuwar akalla fasinjoji 8 da sace wasu sama da 60.

Cikin wata sanarwa da ta fitar jiya a Abuja, hukumar ta ce za a sanar da sabon lokacin da jirgin zai koma aiki, ba tare da ta yi karin bayani kan dalilin dagewar ba. (Fa’iza Mustapha)