logo

HAUSA

Gwamnatin jihar Lagos za ta horar da mata da matasa 150 kan samar da zuma

2022-05-21 17:06:37 CMG Hausa

Hukumomi a jihar Lagos, cibiyar kasuwanci ta Nijeriya, sun ce gwamnatin jihar za ta horar da akalla mata da matasa 150, kan kiwon kudan zuma da samar da zuma da kunshe ta da kuma sayar da ita, domin cike gibin dake akwai a wannan bangare na tattalin arziki.

Kwamishinar kula da aikin gona na jihar Abisola Olusanya, ta bayyana yayin ranar kudan Zuma ta duniya dake gudana a kowacce ranar 20 ga watan Mayu cewa, an kirkiro shirin ne bisa la’akari da yadda ake amfani da ton 380,000 na zuma a kowacce shekara a kasar.

Ta ce alkaluma na baya-bayan nan da ma’aikatar kula da aikin gona da raya karkara ta fitar, sun nuna cewa, ton 15,000 na zuma kadai ake samarwa a kasar, lamarin dake nuna cewa ana shigar da adadi mai yawa na zuma cikin kasar daga kasashen Asiya da Turai.

Kwamishinar ta ce wadanda za su ci gajiyar shirin na gwamnati na samar da zuma, za su samu cikakken horo daga ranar 30 ga wata zuwa 3 ga watan Yuni. Kana za a ba su kayayyakin aiki da dama da za su taimaka musu fara sana’ar cikin sauki.

Har ila yau, ta ce ba taimakawa wajen kyankysar furanni kadai kudan zuma ke yi ba, har ma da taka muhimmiyar rawa wajen kyankyashe amfanin gona, tana mai cewa, idan babu kudan zuma, za a fuskanci karancin amfanin gona. (Fa’iza Mustapha)