logo

HAUSA

Ana nuna ayyukan Huang Yongyu a dakin adana kayayyakin tarihi na Suzhou

2022-05-20 11:01:46 CMG Hausa

Huang Yongyu na karbar bakuncin wani taron nune-nune domin bayyana ayyukansa na zane-zane. An fara nune-nunen ne daga ranar 18 ga wata, wato ranar dakunan adana kayayyakin tarihi ta duniya.

A matsayin wani yunkuri na hadin gwiwa tsakanin dakin adana kayayyakin tarihi na Suzhou da kwalejin fasaha ta Beijing, za a gabatar da ayyuka 78 na Huang da suka hada da zane da sassaka kan icce, dake bayyana nasarorin da ya samu daga shekarar 1940 zuwa 1990.

Huang Yongyu, kwararren mai fasahar zane-zane, na ci gaba da yin tasiri a rayukan rukunonin jama’a, bisa yadda yake bayyana abun dake zuciyarsa cikin ayyukansa.(Fa'iza Mustapha)