logo

HAUSA

Ya dace kasashen BRICS su yi kokarin tabbatar da tsaro da samar da ci gaba ga duniya

2022-05-20 22:01:15 CMG Hausa

A wajen bikin kaddamar da ganawar ministocin harkokin wajen kasashen BRICS da aka yi ta kafar bidiyo da yammacin jiya Alhamis, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi jawabi, inda ya jaddada wasu muhimman batutuwa biyu, dake hade da tsaro da ci gaba, ya kuma nanata cewa, a matsayinsu na kasashen dake bada gudummawa wajen gina duniya, ya kamata kasashen BRICS su tsaya haikan don fuskantar kalubaloli, da tabbatar da zaman karko, da samar da kuzari na raya huldodin kasa da kasa.

Tsaron siyasa muhimmin jigo ne na hadin-gwiwar kasashen BRICS. Tuni shugaba Xi ya gabatar da shawarar tabbatar da tsaron duniya, kuma a jawabinsa na wannan karo, shugaba Xi ya sake nanata muhimmancin shawarar, da bayyana cewa, ya dace kasashen BRICS su kula da muradun juna sosai, da girmama juna a fannoni daban-daban, da adawa da ra’ayin babakare ko kuma mulkin danniya, a wani kokari na gina al’umma mai kyakkyawar makoma ta bai daya a fannin tsaro.

Bugu da kari, wani muhimmin aiki na daban dake gaban kasashen BRICS shi ne samar da ci gaba. Shawarar samar da ci gaba ga duk duniya da shugaba Xi ya bullo da ita, a watan Satumbar bara, ta samu goyon-baya daga kasashe sama da 100, gami da dimbin kungiyoyin kasa da kasa, ciki har da Majalisar Dinkin Duniya. Kuma a cikin jawabinsa a wannan karo, shugaba Xi ya kara da kira da a fadada hadin-gwiwa, da inganta karfin samar da ci gaba.

Duk da cewa annobar COVID-19 na ci gaba da yaduwa, kana kuma tsaron kasa da kasa da murmurewar tattalin arzikin duniya na fuskantar karin kalubaloli, amma muddin kasashen BRICS sun zama tsintsiya madaurinki daya, wajen kula da batutuwan da suka shafi tsaro da ci gaba, da kara samun fahimtar juna a fannin siyasa, da daukar matakai a zahirance, babu tantama za su kara taka rawa a duk duniya, da sanya muhimmin karfi ga ci gaban duniya baki daya. (Murtala Zhang)