logo

HAUSA

Baki biyu bai dace da matsayin Amurka ba

2022-05-19 16:24:51 CMG Hausa

Yayin da gwamnatocin kasashen Sin da Amurka ke kara azamar daidaita tsakani, da shawo kan sabani, da kaucewa mummunar takara, masharhanta na ganin mafi yawan matsalolin da kasashen 2 ke fuskanta na da nasaba ne da yadda Amurka ke karya ka’idoji, ko ra’ayoyin da sassan biyu suka amincewa.

Daya daga muhimman batutuwa dake ci gaba da janyo hankalin duniya, don gane da takun sakar dake wakana tsakanin Sin da Amurka shi ne batun yankin Taiwan na kasar Sin, inda a wasu lokuta Amurka ta sha bayyana goyon bayan ta ga kasancewar yankin Taiwan bangare na kasar Sin da ba za a iya raba shi da babban yankin kasar ba, sai dai kuma a wasu lokuta, matakan zahiri da Amurka ke dauka na nuni da yadda take goyon bayan matakan aware, da ingiza goyon bayan masu burin ballewar yankin na Taiwan.

Idan ba a manta ba, a ranar 18 ga watan Maris da ya gabata, shugaban kasar Sin Xi Jinping, da takwaransa na Amurka Joe Biden, sun zanta ta wayar tarho, inda a tattaunawar tasu aka jiyo shugaba Biden na jaddada matsayin gwamnatinsa na goyon bayan manufar kasancewar yankin Taiwan bangare na kasar Sin. Har ma shugaban na Amurka ke cewa wannan manufa ce da ba za ta sauya ba.

Kazalika a lokacin, Mr. Biden da shugaba Xi sun umarci tawagogin kasashen su, da su gudanar da matakan bibiyar alkawuran da sassan biyu suka yiwa juna, domin tabbatar da ba a sauka daga kan turbar da aka amincewa ba. To sai dai kuma abun tambaya a nan shi ne, shin Amurka ta martaba wannan alkawari da ta yi game da batun Taiwan?

Ga duk mai bibiyar wannan batu, zai lura da yadda sau da dama Amurka ta rika canza matsaya kan wannan batu na Taiwan, ta hanyar tura wakilai yankin, da kulla huldodin ayyukan soji, da cinikayyar na’urorin ayyukan soji ba tare da neman izinin mahukuntan kasar Sin ba. Ko shakka babu, wannan mataki ne da ya saba matsayin Amurka na babbar kasa, da ya dace ta rika kare martabar ta, ta hanyar tsayawa kan alkawuran da ta dauka ba tare da warwarewa ba.

Yin hakan shi ne zai tabbatar da darajar Amurka, na kasa mai karfin fada a ji, tare da maido da dangantakar dake tsakanin kasashen biyu bisa turbar da ta dace, da samun ci gaba mai inganci, da inganta huldar kasashen biyu yadda ya kamata. (Saminu Hassan)