logo

HAUSA

Jakadan Sin dake Nijar ya gana da ministan wajen kasar

2022-05-19 09:49:48 CMG Hausa

Jiya Laraba jakadan kasar Sin dake wakilci a kasar Nijar Jiang Feng, ya  gana da ministan harkokin waje da hadin gwiwa na kasar Hassoumi Massoudou, inda suka yi musanyar ra’ayoyi kan huldar sada zumunta da hadin gwiwa tsakanin kasashensu biyu.

Yayin ganawar ta su, jakada Jiang ya bayyana cewa, huldar dake tsakanin Sin da Nijar tana da kyau, musamman ma yayin da suke kokarin yaki da annobar cutar COVID-19. Kasar Sin tana son hada kai tare da Nijar domin ciyar da huldarsu gaba yadda ya kamata.

A nasa bangaren, minista Hassoumi ya yi tsokaci cewa, duk da cewa, akwai nisa matuka tsakanin kasashen biyu, amma al’ummomin kasashen biyu na da zumunci mai kyau a tsakaninsu. Kuma kasar Sin tana samarwa Nijar tallafi ba tare da gindaya wani sharadi ba, yayin da take kokarin raya tattalin arzikin kasar, musamman ma a farkon barkewar cutar, kasar Sin ta baiwa Nijar taimakon allurar rigakafin cutar ba tare da bata lokaci ba, lamarin da ya taka muhimmiyar rawa a aikin dakile bazuwar annobar a kasar ta Nijar, don haka al’ummun kasar ba za su taba mantawa da tallafin kasar Sin ba har abada. Kana gwamnatin kasar Nijar tana mai da hankali sosai, kan huldar dake tsakaninta da kasar Sin, haka kuma tana daukar kasar Sin a matsayin muhimmiyar abokiyar hadin gwiwa, tana kuma son hada kai da kasar Sin domin ciyar da huldar hadin gwiwa da sada zumunta dake tsakaninta da kasar Sin gaba lami lafiya. (Jamila)