logo

HAUSA

Jakadan Sin ya yi kira a bada fifiko wajen bunkasa ci gaban yankin Sahel

2022-05-19 13:10:02 CMG Hausa

Wakilin kasar Sin ya bukaci a bada fifiko wajen bunkasa cigaban yankin Sahel. Zhang Jun, zaunannen wakilin kasar Sin a MDD, ya ce Afrika tana fuskantar wahalhalu wajen cimma nasarar samun cigaba. Matsalolin karancin abinci da duniya ke fuskanta a halin yanzu, da matsalar makamashi, da ta kudade, sun kara tsananta halin da ake ciki a Afrika, sannan matsalar ta fi kamari a yankin Sahel.

Zhang Jun, ya bayyana hakan ne a yayin taron kwamitin sulhun MDD game da shirin G5 Sahel, wato wani shiri ne na hadin gwiwa don tsara manufofin bunkasa cigaba da tabbatar da tsaron yammacin Afrika.

Jakadan na kasar Sin a MDD ya bayyana cewa, MDDr tana shirin tsara muhimmin shirin bincike na hadin gwiwa tare da kungiyar tarayyar Afrika AU, da kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika wato (ECOWAS), da yankin Sahel. Ya ce ana fatan MDD za ta karfafa tuntubar juna tare da dukkan masu ruwa da tsaki wajen cimma wannan shiri, da nufin zurfafa goyon bayan juna, da hadin gwiwa a tsakanin kasashen shiyyar.

Da yake karin haske game da hadin kai da hadin gwiwa, Zhang ya ce, babu wata kasa da za ta iya magance wadannan kalubaloli ita kadai. Ya kamata kasashen shiyyar su karfafa goyon bayan juna, da hadin gwiwa, tare da tallafin kasa da kasa, domin fito da matakan tinkarar matsalolin ta hanyar hadin gwiwa. (Ahmad)