logo

HAUSA

Bankin bada rance na Afrika ya bukaci a bunkasa matsakaitan birane don dakile kaura birane

2022-05-19 13:10:54 CMG Hausa

Babban jami’in bankin samar da rance na Afrika AfDB ya ce, kamata ya yi kasashen Afrika su bunkasa muhimman kayayyakin more rayuwa kamar gidaje, da ilmi, da samar da ruwa mai tsafta, da kiwon lafiya, a matsakaitan biranen nahiyar Afrika domin bunkasa ci gaban yankunan ta yadda za su taimaka wajen dakile kwararar mazauna karkara zuwa birane.

Babati Mokgethi, babban jami’in sashen bunkasa birane na bankin bunkasa ci gaban Afrika AfDB, ya ce ya kamata a dauki matakan karkatar da akalar adadi mai yawa na mazauna yankunan karkarar Afrika zuwa matsakaitan birane, domin rage tsananin cunkoson da manyan biranen nahiyar ke fuskanta. Ya bayyana hakan ne a gefen taron kolin Africities wanda ke gudana a birnin Kisumu dake yammacin kasar Kenya.

Mokgethi ya bayyana cewa, zuba jari a matsakaitan birane zai taimaka wajen samun bunkasar tattalin arziki a yankunan karkarar Afrika, kana matakin zai taimaka wajen samar da sana’o’i da ayyukan yi, wadanda za su dakile kwararar mutanen dake zuwa biranen don neman ayyukan yi.

Ya ce, matsakaitan birane wadanda sun kasance wuraren zama ga kashi 15 bisa 100 na yawan al’ummar Afrika, suna bukatar a samar musu da ingantaccen tsarin sufuri na zamani, da tsaftataccen ruwan sha, da gidajen kwana masu saukin kudi, don kyautata rayuwarsu. (Ahmad)